1 ¶ Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar.
2 “Ku ne kaɗai na zaɓa cikin dukan al’umman duniya; saboda haka zan hukunta ku saboda dukan zunubanku.”
3 Mutum biyu za su iya yin tafiya tare in ba su yarda su yi haka ba?
4 Zaki yakan yi ruri a jeji in bai sami kama nama ba? Zai yi gurnani a cikin kogonsa in bai kama kome ba?
5 Tsuntsu yakan fāɗa a tarko a ƙasa inda ba a sa tarko ba, ko tarko yakan zargu daga ƙasa in ba abin da ya taɓa shi?
6 Idan aka busa ƙaho a ciki birni mutane ba sa yin rawar jiki? Sa’ad da bala’i ya auko wa birni, ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba?
7 Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.
8 Zaki ya yi ruri, wa ba zai tsorata ba? Ubangiji Mai Iko Duka ya yi magana, wa ba zai yi annabci ba?
9 Ku yi shela ga kagarun Ashdod da kuma ga kagarun Masar. “Ku tara kanku a tuddan Samariya; ku ga rashin jituwar da take a cikinta, da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.”
10 “Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,” in ji Ubangiji, “sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.”
11 ¶ Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Abokin gāba zai ƙwace ƙasar, zai saukar da mafakarku, zai washe kagarunku.”
12 ¶ Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya, haka za a ceci Isra’ilawa, masu zama a Samariya da kan gado kawai da kuma a ɗan ƙyalle a kan dogayen kujerunsu.”
13 ¶ “Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki.
14 “A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta, zan hallaka bagadan Betel; za a yayyanka ƙahonin bagadan za su fāɗa ƙasa
15 Zan rushe gidan rani da na damina; gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,” in ji Ubangiji.